YAR RAWA SABON LITTAFI PART 3 - AREWAJOB

KUNDIN AYYUKA AREWAJOB

Breaking

ads

Saturday, 5 January 2019

YAR RAWA SABON LITTAFI PART 3

              YAR RAWAR KASHI NA 3


cigaban sabon littafi mai suna yar rawa kashi na biyu 


Dakin Delu suka shiga suka zazzauna, ta je ta debo masu abincin da Ameenee ta dafa, da ruwa mai sanyi, rabon su da cin abincin gidan dan uwan nasu tun zamanin Tabawa, shekaru biyu kenan, amma yau har da ruwan randar sanyi, tasa daga yaranta suka siyo mata balangu ta watsa masu akai, aiko kamar mayu haka suka hau abincin da ci, ga shi dama Ameenee a yan shekarun ta ba dai iya girki ba, tunda kullum ita takeyi, na safe , na rana, na dare, duk itace dole ta kware. Bayan sun kammala ne ta daya daga cikin su mai suna Bappa Lado wanda yafi kowa baqar zuciya yace, "Delu kin aika a kira mu ina fatan kiran mai amfani ne, dan ni kan na fito aike ya iskeni daga mai gari gaba dayan mu da yan uwana mu je fada akwai mahimmin abu daya taso, dan haka ina ganin ku da baku sani ba yanzu na isar muku, sai mu qoqarta mui hanzari mu kammala na nan mu je can muji me ya taso haka na gaggawa?" Gara zama tai ta ce " ba komai ne yasa na kira ku ba Lado face maganar auren yaeinyar nan da mai gari keson yi, ni fa ba na son marainiyar Allah ta bar gabana, ta bar garinnan kwata2,..... sai ta fara kukan munafurci harda fyace majina.... in ta tafi Lado ban san halin da take ciki ba akwai damuwa da zata sarqen, ina tsoron nima na rasa raina saboda rashin Malam da diyar shi, sannan mutumin nan da gani ba dan Nigeria bane, wa yasan sana'ar shi, kuma malam bai da rai bare ace ya tabbatar zai bada ita a yanzu, babban kuma wani abun dubawar yarinyar nan bata son shi, tana ganin shi ma kuka ta saka" tsagaitawa tai tana kuka sosai kamar na gaske, tausayin ta ne ya kama wasu daga cikin su, wasu kuma suna ganin anya??? Lado shi anashi bangaren ba ruwan shi da koma me zai sami yarinyar tinda Delu bata son auren to fa ba wanda ya isa daura shi, " kiran mai gari na da nasaba da zuwan yaron ya kamata ku hanzarta kar mai afkuwa ta afku, ku tai maken da yar ku da dan uwan ku" kuka ta qara sakawa mai cin rai ita a dole kar a cutar da marainiya, miqewa suka suka kama hanyar gidan mai gari suna tattauna yanda zasu bullowa lamarin.

A fada waje ya cika ba laifi dan sanar da jama'a me za ai da me gari ya saka a yi, suna isa mai gari ya shigar da su wani daki, harda Aminin Malam wato Malam Abubakar, sai kuma su El-mustapha da Mus'ab abokin shi, zama sukai mai gari yai addu'a suka shafa sannan yace" Malam Lado na sa an kira ku ne da yan uwan ka akan batun auren Ameeaatou, meye ra'ayin ku akan wasiyyar dan uwan ku na a a aura ma wannan bawan Allah ita ko bayan ran shi?" " Ranka ya dade ni na ke bin tsohon wannan yarinya, nasan abinda yake so da wanda baya so, dan haka gaba daya wancan karon wannan bawan Allah tilasta mai yai akan ya aura mai ita,ba dan ya so ba ya amince, kan ya mutu ni da shi munyi wannan maganar," cikin kidima El-mustapha ya ja baya yana zare ido da dafe qirji kamar wata budurwar da ta shiga damuwa, yace" Malam Ka ji tsoron Allah, kaji tsoron ranar da Allah zai tsaidaka ka maimaita abinda kace, kaji kunyar ranar da zaka maimaita wannan qaryar gaban dan uwan ka, wannan abun da ka fada bai faru ba, ba a taba yin shi ba, yarinya bata taba cewa tana sona ba ni na ce ina son ta,amma da dikkan alamu itama tana sona, ni ban taba furta mata kalmar so ba, na kula qarama ce tai qanqanta da hakan, dalilina na zuwa nansamu mahaifinta kenan, dan hakan shine mafi dacewa, uba na da damar zabawa yarinyar shi mai auren fari miji, musamman wannan da bata san komai ba" sunkuyar da kan shi yai yana hawaye,badan komai ba ganin yau ba Malam Muhammad ana neman shiga tsakanin shi da abar son shi , baida kowa a duniya, ita yake saka ran ta zama mai komai, ta maye mai gurbin rashin iyaye da yan uwan kirki da yai, amma gashi komai na neman zama mai ba daidai ba, kafadar shi yaji an dafa da sigar lallashi, " ka kwakntar da hankalin ka, wannan aure kamar anyi an gama ne, ba wanda ya isa ya daga shi, domin kuwa ni ne aminin mahaifin ta.ni da shi ya tabbatar min ya baka ko bayan ranshi ka dawo ai wannan aure naku ga mai gari shaida n3 shima"mai gari ne ya qara tabbatar ma shi hakan shima,nan take kwanciyar hankalin shi ta bayyana " ammmm bayin Allah ban katse maku hanzari ba, amma in dai za ai auren nan ba yawun mu, ko shekara dari zamu sake.a duniya in dai akai auren nan ba mu ba Ameenaa ba zuri'ar ta, tinda mu yan uwan mahaifin ta an mai damu bamu da amfani," inji na Duduwalle kenan daya daga Bappanin ta, me gari ko sauraran su bai sake yi ba ya baza babbar rigar shi ua fito suma si malam Abubakar suka bi shi, nan take aka daura auren su, akan sadaki dubu 20k, cikin farin ciki, Malam Abubakar ne ya wakilce ta shi kuma Mus'ab shine ya wakilce shi, haka akai auren cikin saka albarkar mutane da yawa,kamar sun san za ai auren dama can yanda aka taru a wajen, fakam fakam fakam suka zo suka wuce suna huci, bayan an dunqula masu goro da alawa a ledoji, ba kunya suka amshe sukai gidan Delu, suna zuwa daga yanayin su ta gane an gama komai, hannu ta dora aka ta rusa kuka, " shikenan sun cuce ni sun cuci marainiyar Allah, in dai ina nunfashi yarin yar nan ba za ta bar gidannan ba, sun ganta marainiya za su cutar da ita?" Daidai nan su Malam Abubakar suka iso, " zamu cutar da ita ko kk cutar da ita kuma kk shirin qara cutar ta? Dwlu duk makircin ku akan idona kk aikata shi, tin fil azal, ki kiyayeni dan wannan karon ba auren aminina akan ki ba zan dau iskancin ki ba," " Malam Abu ka duba fa ka gani auren dole kuke son yi wa marainiya ko nace kukao ma marainiya"ta fashe da kukan baqin cikin halin hutun da ya zo wa Ameenee, ki ra Malam din yai ta banka mata, nan da nan ta iso da hanzari ta duqa kan ta a qasa, ta gaida su ta dada takurewa gefe, dan a yanzu duk ta fuskanci inda zantukan su suka saka gaba, " Ameenaatou, kina son wannan bawan Allah ko baki son shi, ki fadan gaskiya kamar yanda zaki fafa ma marigayi, ni ubane a wajen ki , ko da wadannan ubannin naki sun juya maki baya ni ina nan tare da ke har qarshen nunfashina" hawaye take sosai, na fahimtar kenan su Bappanin ta sun qi ta ne, gefen da gogan nata yake ta kalla qasa qasa, cikin sa'a idon su ya hadu, wani marairaice mata yai akan ta amince da shi, murmushi ne ya subuce mata shima hakan, ta qara sunkui da kai tana rufe fuska, malam ne ya ce" to Alhamdu lilLAAH ina ganin wannan kadai ya baku amsa dan haka Ameenee debo kayan ki mu wuce gidana da ke da mijin ki cam zaku kwana kafin tafiyar ku jibi, domin ni ba kowa garen ba kun sani iyalina ta mutu kuma Allah bai bamu haihuwa ba, akwai wajen da zai ishe ku ku kwana kai da abokin ka da iyalin ka, mu tashi mu wuce, ke kuma Allah ya shirye ki da ku baki daya ku gane meye ma'anar zumunci" Bappa Lado ne ya karkata baki yace" Ameeeen da bamu san akan me kk wannan rawar jikin bane da sai mu zaci kai ma dan zumuncin kayi" Malam bai kula shi ba, haka suka jira ta ta debo kayan ta suka wuce gidan malam din, daki daya aka ware masu mai katifa da ledar daki, shikenan sai dan bargo da zanin gado, anan aka sauke su, Mus'ab ma dakin nashi haka ne, bayan sun isa ne, El-mustapha ya sanar da malam gobe zasu wuce, malam ya musu fatan alkairi da addu'o'i Ameenee ta sha kuka sosai, inda tin yana lallashin ta shima ya saka mata kukan,tin da shima yau ce rana abar baqin ciki a tare da shi, yayi auren fari ba kowa na shi, ga matar da yake so itama tana cikin damuwar, rungume ta yai suka sha kukan su a hakan,.

Washe gari su Ameenee an dau hanyar tafiya Niger, a hanya ta sha bacci sosai, suna isa gidan su kuwa Mus'ab ya musu sallama ya tafi gidan shi, shima, nan take ya aika da driver aka kai ma su abinci da abubuwan dai da zasu buqata a ranar, sannan ya aika wata daga cikin masu aikin shi, yar dattijuwa yace taje ta kula da Ameenee, ta kuma koya mata abubuwan da duk ya kamata ta iya, dan shi mai suna, Ameenullahi ne ke ta kuka, sai ya bi Iya gidan da zata dan sun shaqu sosai, hakuri ta bashi tace zata dawo nan da kwana  biyar su tafi, Ameenullahi mai shekaru 6 a duniya ga wayo, yasan ba ta mai qarya sai ya hakura amma hawaye bai bar zuba mai ba, tafiya tai, aka kaita tana zuwa,ta isa inda Ameenee take ta kwashi gaisuwa, nan da nan Ameenee ta zube a qasa itama, ganin babbar mata da ta kusa sa'ar Innar ta tana duqawa tana gaida ta, gaisawa sukai a haka, El-mustapha da ya shigo ya gansu dariya ta kama shi, yai tayi kuwa, isa yai gabam Ameenee ya dago ta ta dan jamye kadan ganin wannan dattijuwa na wajen, sannan ya umarci Iyan da ta tashi, tashi tai ta zauna akan kujera kamar yanda ya umarta " da farko dai Iya wannan iyalina ce, sunan ta Ameenaatou, Ameenee wannan ita ce zata na zama dake musamman in bana nan, kuma kina buqayar wani abu duk zata maki, zata na taya ki ayyukan gida, ta koya maki abubuwan da baki iya ba, ina fatan ba matsala, ke kuma Iya daga yau kina dauki Ameenee kamar 'ya, sai dai kawai ba zan lamunci muzguna mata ko bata ranta ba a wajen kowa, dan wannan girman da kk bata ita ta taso gian tarbiyya ba zata so shi ba ina fatan kin gane" kada kai tai tare da godiya, ya nuna mata bangaren da zata zauna ya ja hanun iyalin shu suka tafi, a yau din komai ya wakana tsakanin shi da iyalin shi, wanda ya danganci amarci da raya sunnar ma'aiki, su Ameenee an sha fama da maza😱🙊 tayi kuka hr ta gode Allah sai da yace mat " in kina kuka Iya zata gane me mukai, ki shiru kae kowa ya ji, a maki dariya ke raguwa ce, in miji na ma matar shi haka lada suke samu, amma in wanda ba miji da mata bane zunubi suke samu, na san a karatun ki kin san hakan ai ko? Daga mai kai tai yace yauwa Habibaty, ku daina kuka, daga yau ba zan qara maki wanda zai saki kukan wahala ba kinji" daga mai kai tai, nan take suka tashi suka tsarkake jikin su kafin suka koma bacci,( ana son mutum bayan ya kusanci iyalin shi sui wanka ba a son kwana da janaba) bacci mai dadi sukai.

Washe gari ta tashi da tsamin jiki,musamman cinyoyin ta, ruwan zafi sosai mai hadin kayan qamshi na musk, da magarya,sai yar bagaruwa kadan, da kaninfari iya ta kawo mata tace ta shiga ta zauna zata daina jin ciwon jiki, nan da nan ta zaro ido😳😳😳😳ko dai iya tasan me akai jiya ne,wata kunya ce ta kama ta ta daqe bakin ta ta kama tafiya a tsaye da sauri tana son ta gudu daki, yana hango su ta parlo dariya ta gama cika mai ciki,tashi yai ya amsa yai mata godiya ya kai mata ruwan, samun ta yai bakin gado tana hawaye " Ya salam me ya same ki Ameenee na? Wa ya bata ran sahiba ta,? Ko dan iya ta baki wannan ne baki so, bata gane komai ba fa, kawai tasan kin gaji tafiyar hanya ne yasa ta miki wannan hadin, da kin shiga robar kk zauna zakiji dadi a jikin ki," kallon shi tai da idanun ta masu kyau da sukai ja, kada mata kai yai alamar da gaske bata gane komai ba, cikin ran shi kam dariya ce cike, tqna shiga ko ya fashe da dariyar, yace " ikon Allah, ashe haka auren yara yake?" .........

No comments:

Post a Comment