{JAMB 2019} WASU DAGA CIKIN AMSOSHIN LITTAFIN SWEET SIXTEEN - AREWAJOB

KUNDIN AYYUKA AREWAJOB

Breaking

ads

Saturday, 9 February 2019

{JAMB 2019} WASU DAGA CIKIN AMSOSHIN LITTAFIN SWEET SIXTEEN


A Shekarun Baya, Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’a wato Jamb ta sanya littafin SARAH LADIPO SOYINKA a matsayin Littafin da dalibai Zasu karanta. amma a shekarar ta bana 2019 ta sanya littafi mai suna  SWEET SIXTEEN wallafar BOLAJI ABDULLAHI wanda acikinsa ne JAMB zata tsarma musu tambayoyin yaren Turanci.

Mun bincike mun kuma zakulo muku wasu tambayoyi da zasu iya kasancewa cikin tambayoyin da zasu zo daga littafin, mun kuma kawo muku su da amsoshinsu cikin harshen Hausa domin ku dalibai:

kadan daga ciki sune:

Wacece Aliya?

Aliya itace jigon labarin littafin Sweet Sixteen, ita kadaice a wurin iyayenta, tana samun kulawa sosai, tana da kusanci sosai da mahaifinta, sai dai tana fuskantar wasu kalubale a makaranta.Waye Mr. Bello?

Mr. Bello shine mahaifin Aliya, Dan Jarida ne, yana bala’in sonta sosai, don haka ya zuba idanunsa akanta qwarai da gaske.


Wacece Mrs. Bello?

Mrs. Bello itace Mahaifiyar Aliya matar Mr. Bello.


Wacece Big Mummy?

Big Mummy itace kakar Aliya, Mahaifiyar Mr. Bello, Surukar Mrs. Bello Kenan.


Wacece Aunty Molara?

Aunty Molara kanwar Mrs, Bello ce mahaifiyar Aliya, Kenan ita kanwar babar Aliya ce (Aunty).


Wanene Principal?

Tsoho ne sosai idan muka kwatantashi da Mr. Bello baban Aliya, amman ya zama aboki sosai a wurin baban Aliyan, Principal Christa ne dan kabilar TIV.


Wanene Bobo?

Bobo dan ajin su Aliya ne a makaranta, shine wanda yayi mata kyauta a ranar masoya wato (Valentine’s Day), ya taba zuwa bakin ruwa tare da wata Budurwa mai suna Morayo.


Waye Akin?

Akin dan Ajin su Aliya ne a makaranta, dalibine mai kokari/kwazo sosai da sosai, sannan yana da yawan abin dariya da nishadi.


Wacece Miss Salako?

Miss Salako itace Malamar Lissafi (Mathematics), wadda ta hukunta Akin  saboda yazo da wasa alokacin da take darasi a aji.


Waye Bunmi?

Shi kuma dan makarantar su Aliya ne, amman ya wucesu a aji, kuma shine mai tsokana/kyarar Aliya a makaranta.


Wacece Malamar Biology?

Malamar Biology tana yabon Aliya, sunan malamar shina Fatima


Waye Zak?

Zak dalibine mai kokari wanda ana alfahari dashi a makarantar, shine ya baiwa Aliya  rubutaccen sakon soyayya.


Wace Grace?

Grace dakinsu daya da Aliya bata da yawan magana, mutane na mata kallon girmankai da wulakanta mutane.


Wacece Bisi?

Itace yarinyar da ta dage wajen ganin ta hana Aliya zuwa ofishin Principals.


Waye Sogo?

Sogo ‘yar ajin su Aliya ce mahaifinta yace sai tazama Lawyer tunda shima Lawyer ne


Domin Shawara mu hadu a shafin sada zumunta:
FACEBOOK
INSTAGRAM

Domin Samun Videos Masu Kayatarwa kayi subsribe a Arewajob TV


                                                                CLICK HERE TO SUBSCRIBE

No comments:

Post a comment