SAURA KWANA 4 ZABE OFISHIN INEC YAYI GOBARA YA ABUN YAKE NE?? - AREWAJOB

KUNDIN AYYUKA AREWAJOB

Breaking

ads

Monday, 11 February 2019

SAURA KWANA 4 ZABE OFISHIN INEC YAYI GOBARA YA ABUN YAKE NE??

An kona daya daga cikin ofishin hukumar zabe a Najeriya kwanaki shida kacal kafin gudanar da babban zabe a kasar.
Gobarar dai ta faru ne a ofishin hukumar a jihar Filato dake arewacin kasar inda muhimman kayayyakin zabe kamar akwatuna da takardun jefa kuri'a suka kone.
Mai magana da yawun hukumar ya bayyana kona ofishin a matsayin mayar da hannun agogo baya a bangaren shirye-shiryen zabe

A wata sanarwa da hukumar zaben ta fitar ta bayyana cewa wannan ne karo na biyu da aka samu konewar ofishinta a cikin wannan watan, inda tayi kira ga jami'an tsaro a kasar da su kara matse kaimi wajen ba ofisoshinsu tsaro.
Ana sa ran dai za a gudanar da babban zabe a kasar a ranar Asabar.
A ranar lahadi ne dai shugaban kasar Muhammadu Buhari yayi gargadi a kan magudin zabe.
A wani bangaren kuma, shugaban ya koka a kan zargin da hukmar EFCC a kasar tayi na makudan kudaden da ake fitarwa ba bisa ka'ida ba domin siyan kuri'a.

No comments:

Post a comment