Mun samu labari cewa wasu sun fara kira a dakatar da ‘dan takarar
jam'iyyar PDP na shugaban kasa a zaben 2019 watau Alhaji Atiku Abubakar
daga takara inda ake zargin cewa ba a Najeriya aka haife sa ba.
Wasu na ikirarin a wajen Najeriya aka haifi Atiku Abubakar
Dr.
Bunmi Awoyemi yayi wani rubutu a cikin makon nan inda yake cewa Atiku
Abubakar ba haifaffen ‘Dan Najeriya bane. Marubucin yace an haifi Atiku
ne a wani karamin gari ne da ake kira Jada wanda a da yankin na cikin
kasar Kamaru.
Sai bayan an haifi Atiku Abubakar
da dadewa ne sannan yankin Jada da kewaye na Arewacin kasar Kamaru su
ka shigo cikin Najeriya. Wannan ya sa wasu ke ganin cewa dokar kasar nan
ta haramtawa Atiku tsayawa takara a Najeriya.
A
tsarin mulki, bai halatta mutum ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa
ba, har sai idan an haife sa a Najeriya. Kauyen da Atiku Abubakar ya
fito kuwa bai zama cikin Najeriya ba sai kusan bayan yayi shekaru 15 da
haihuwa a Duniya.
Haka zalika kuma dokar
Najeriya na cewa kafin mutum ya zama haifaffen ‘dan Najeriya, dole ya
zama cewa an haife sa ne a cikin kasar kafin samun ‘yancin kai. Najeriya
ta samu ‘yancin kai daga mulkin mallaka ne a farkon Oktoban 1960.
Sai
dai tuni kuma Masana irin su Abdul Mahmud wanda kwararren Lawya ne yayi
kaca-kaca da wannan magana inda yace yankin na Adamawa da ma kasar
Taraba ba su taba shiga cikin tsantsar kasar Kamaru a wancan lokaci ba.
No comments:
Post a Comment